Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci Afrika ta gyara dokoki don inganta tsarin biyan harajin tattalin arziki na zamani
2019-10-02 15:47:26        cri

A jiya Talata MDD ta bukaci kasashen Afrika da su gyara dokokinsu da nufin inganta tsarin biyan haraji na kudaden shigarsu a fannin tattalin arziki na zamani.

Uzumma Marilyn Erume, jami'ar sashen tattalin arziki a hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD ta bayyana wa manema labarai a Nairobi cewa, fannin tattalin arziki na zamani a Afrika yana samun saurin bunkasuwa da kusan kashi 40 bisa dari a duk shekara.

A cewarta, akwai bukatar kasashen Afrika su gudanar da sauye sauye a tsarin biyan harajinsu domin gwamnatocin kasashen su samu damar tattara kudaden shiga a fannin tattalin arziki na zamani, Erume ta bayyana hakan ne a gefen taron kasashen Afrika karo na 7 game da batun karkatar da kudade ta barauniyar hanya da batun biyan haraji.

Taron na wuni uku na shekara shekara, ya tattaro kwararrun masana tsara dabarun ci gaba, da malaman jami'o'i, da kungiyoyin fararen hula daga kasashen Afrika domin sake bibiyar hanyoyin yaki da zambar kudade da yadda za'a inganta albarkatun da ake samu na cikin gida a nahiyar.

Erume ta ce, Afrika yanki ne mafi koma baya ta fuskar biyan haraji na tattalin arzikin da ake samarwa na cikin gida wato GDP a duniya baki daya.

Ta bukaci nahiyar da ta kara zakulo fannoni da za'a kara fadada hanyoyin samun kudaden shiga ba tare da haifar da wata barazana ga yanayin tattalin arzikin cikin gidan kasashen ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China