Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su zamanantar da tsarin yi wa jama'arsu rajista
2019-08-10 15:54:11        cri

Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD ECA, ta bukaci kasashen nahiyar, su zamanantar da tsarin yi wa jama'a da muhimman bayanansu rajista, domin samun ingantacciyar al'umma da ta kunshi kowa da kowa.

Daraktan cibiyar kididdiga a hukumar ECA, Oliver Chinganya ne ya yi kiran a jiya, yayin da nahiyar ke bikin ranar rajistar jama'a da muhimman bayanansu, karo na 2 a yau Asabar, wanda aka yi wa taken "Takardar Shaidar Haihuwa ga Kowa: Ginshikin Kare Hakkin Dan Adam da Tafiya tare da Kowa".

Hukumar ECA ta yi kiyasin sama da mutane miliyan 500 a fadin nahiyar Afrika ba su da katin shaidar dan kasa, kuma daga cikinsu, akwai yara miliyan 120 da ba su da takardar shaidar haihuwa.

Sanarwar da hukumar ta fitar jiya, ta ruwaito Oliver Chinganya na cewa, takardun shaidar haihuwa na taimakawa wajen shiga makaranta, da samun hidimomin kiwon lafiya da kare al'umma, wanda ke rage raunin yara ga talauci da cin zarafi. Ya kara da cewa, rajistar haihuwa muhimmin batu ne ga tsarin rajistar rayuwar mutum, kana hakki ne na dan Adam, kuma yana inganta batun shigar da jama'a cikin shirye-shiryen raya al'umma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China