Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jaddada bukatar hada shirye-shiryen Afrika da BRI don samar da ababen more rayuwa
2019-07-08 09:25:04        cri

Mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohammed, ta jaddada muhimmancin hada shirye-shiryen ci gaba na nahiyar Afrika da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin BRI, domin samar da ci gaba a fadin nahiyar.

Da take bayyana kudurin MDD na aiki da cibiyoyin nahiyar wajen samar da abubuwan da ake bukata don aiwatar da yarjejeniyar ciniki mara shinge (AfCFTA), wadda ta fara aiki a jiya Lahadi, Amina Mohammed ta jaddada bukatar zuba jari a bangaren ababen more rayuwa, idan har nahiyar na son cin gajiyar alfanun dake tattare da yarjejeniyar.

Yayin bude taro na 12 na shugabannin kasashe mambobin Tarayyar Afrika jiya a Niamey, babban birnin Niger, Amina Mohammed ta ce MDD za ta yi aiki da shugabannin Afrika domin samar da hanyoyin samun kudi daga asusun bankin raya nahiyar Afrika, zuwa shirin AU na samar da ababen more rayuwa a nahiyar da kuma shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China