Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD za ta taimakawa Afirka tsara manufofin da za su saukaka kaurar jama'a
2019-09-24 09:53:56        cri

Hukumar kula da kaurar jama'a ta MDD, ta bayyana kudirinta na taimakawa kasashen Afirka tsara manufofin da za su saukaka kaurar jama'a.

Jami'ar shiyya ta hukumar mai kula da tsara manufofi Alice Kimani ce ta bayyana hakan, yayin taron dandalin kula da kaurar jama'a na shiyya da aka shirya a birnin Nairobi na kasar Kenya. Ta ce, kasashe da dama, ciki har da Kenya da Sudan ta Kudu da Habasha da Uganda sun bukaci neman taimako.

Kimani ta ce, za su taimakawa kasashen Afirka da dabarun sanin makamar aiki, ta yadda kasashen za su tsara managartan manufofin da za su tabbatar da kaurar jama'a kamar yadda aka saba ba tare da wata matsala, ta yadda za su ba da tasu gudummawar ga ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a a nahiyar.

A nata bangare, hukumar ta MDD, za ta taimakawa kasashen na Afirka, kulla yarjejeniyar kwadago a tsakanin kasashen da 'yan gudun hijirar suka fito da kasashen da suka nufa, don neman aikin yi, ta yadda za a kare musu 'yanci da mutuncinsu bisa doka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China