Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#China70# Xi Jinping: Ba wanda zai hana ci gaban kasar Sin
2019-10-01 10:31:48        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, yanzu haka kasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman, ta sha kan gabashin duniya yadda ya kamata, ba wanda zai iya hambarar da ita, kuma ba wanda zai iya hana ci gaban jama'ar Sinawa da al'ummarsu.

Xi Jinping ya nuna cewa, kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin ya canja halin da kasar ke ciki, a zamanin kusa na rashin samun bunkasuwa da koma baya da karancin wadata, hakan ya sa, Sin ta kama wata hanya da ta dace da samun farfadowa.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, al'umomin daban-daban na kasar Sin na kokarin hada kansu, da yi kokari tare don samun ci gaba mai armashi, matakin da ya baiwa dukkanin kasashen duniya mamaki matuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China