Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da shugaban tawagar Afirka
2019-06-24 14:51:15        cri
A yau Litinin a nan birnin Beijing, mataimakin shugaban kasar Sin, Wang Qishan ya gana da shugaban tawagar wakilan Afirka da suka halarci taron bin diddigin yadda ake tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar a birnin Beijing.

Wang Qishan ya ce, taron ya kasance wani muhimmin mataki da aka dauka na tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin da aka gudanar a watan Satumban bara, wanda kuma ya kasance wani babban al'amari a huldar dake tsakanin Sin da Afirka, ya kamata sassan biyu su yi ta yin musayar ra'ayoyi da juna da hada gwiwa da juna.

Shugaban tawagar wakilan Afirka a nasa bangaren ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka ya zama misali ta fannin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Afirka ta yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma, kuma tana fatan ganin hada kanta da kasar Sin wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya", don tabbatar da nasarorin da aka cimma a taron kolin da aka kira a bara.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China