Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Sin ta dauki kwararan matakan hana fasa kwaurin namun daji na Afrika
2019-08-24 15:59:47        cri
Sabon rahoton da cibiyar nazarin tsaro ta ISS ta wallafa ya nuna cewa, kasar Sin tana cigaba da daukar kwararan matakan yaki da fasa kwaurin namun daji daga nahiyar Afrika, kuma a 'yan shekarun baya bayan nan matakan sun taimaka wajen raguwar laifukan da suka shafi fasa kwaurin dabbobin daji a Afrika.

Cibiyar ISS, wata kungiya ce mai zaman kanta dake Afrika, a cikin rahotonta na mako-mako data wallafa a kwanan nan ta bayyana cewa, tun a shekarar 2017 kasar Sin ta rufe dukkan wasu kasuwanninta na cikin gida wadanda ake hada hadar hauren giwa, kana ta haramta sarrafawa da cinikin kahon karkanda da kasusuwan damisa.

Haka zalika rahoton yace, kasar Sin ta tsaurara dokokinta game da harkokin ciniki da suka shafi dabbobi da tsirrai da ke dab da karewa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China