Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude muhawarar babban zauren MDD
2019-09-25 10:26:23        cri

An bude muhawarar babban zauren MDD karo na 74 a jiya Talata, inda aka yi masa taken "karfafa yunkurin kasa da kasa domin kawar da talauci da samar da ingantaccen ilimi da kiyaye yanayi".

Shugaban zauren na 74, Tijjani Muhammad-Bande ne ya jagoranci bude muhawarar, inda ya yi kira da a hada hannu wajen magance kalubalen da duniya ke fuskanta, ta hanyar ba da muhimmanci ga muradun ci gaba masu dorewa.

A jawabinsa, sakatare janar na majalisar, Antonio Guterres, ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya, su rika sanya muradun al'umma a gaban komai. Ya ce kalmomin farko na kundin tsarin majalisar wato "mu mutane", na kira ne da sanya al'umma matsayin jigon dukkan ayyuka a kullum, kuma a ko ina.

Jimilar shugabannin kasashe 91 da shugabannin gwamnatoci 45 tare da wakilansu a matakai daban daban ne suka nemi yin jawabi a kan mumbarin zauren majalisar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China