Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yabawa hadin gwiwarta da Sin da gudunmuwar da kasar ke ba ta
2019-09-21 15:32:56        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yaba da hadin gwiwar majalisar da kasar Sin da kuma gudunmuwar da kasar take ba ta.

Antonio Guterres, ya bayyana haka ne gabanin da kasar Sin ke cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar al'ummar kasar Sin a ranar 1 ga watan Oktoba.

Sakatare janar din ya ce, kasar Sin na taka gagagrumar rawa a ayyukan majalisar, kuma ta kasance ginshikin hadin gwiwa da dangantakar kasa da kasa, yana mai cewa, MDD da kasar Sin suna ci gaba da aiki tare domin magance batutuwan dake ciwa duniya tuwo a karya.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne cikin wani sako da mataimakiyarsa Amina Mohammed ta karanta, yayin wata liyafa da wakilcin dindindin na kasar Sin a MDD ya shirya domin bikin ranar kafuwar Jamhuriyar kasar Sin.

Har ila yau, Antonio Guterres ya bayyana fatan aiki da kasar Sin kan sauyin yanayi. Ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance wadda ta fara aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa na majalisar. Ya ce a matsayinta na kasa ta 2 mafi bayar da gudunmuwa ga shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na majalisar, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen hulda da majalisar ta hanyar tabbatar da ta na iya gudanar da ayyukanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China