Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron MDD ya amince da yarjejeniya a siyasance kan yadda za a inganta samar da kiwon lafiya a matakin farko
2019-09-24 13:44:32        cri

A jiya ne taron manyan jami'an MDD, ya amince da yarjejeniya a siyasance kan yadda za a kara fadada matakan kiwon lafiya a matakin farko a duniya, matakin da ke nuna kudirin shugabannin kasashen duniya, na kara samarwa al'ummominsu matakan kiwon lafiya a matakin farko.

Kundin ya kunshi, yadda karin mutane biliyan daya za su ci gajiyar shirin nan da shekarar 2023, ta hanyar samun kulawar lafiya mai inganci, da tsaro da muhimman magunguna masu rahusa, alluran riga kafi, da binciken lafiya da fasahohin lafiya na zamani, da yadda shirin zai karade dukkan al'ummomi nan da shekarar 2030.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba da yarjejeniyar, da ya bayyana ta a matsayin "mafi dacewa da aka cimma kan harkokin kiwon lafiya a duniya". Ya kuma bayyana ta a matsayin mai muhimmanci a kokarin da ake na samar da lafiya ga kowa da kowa.

Mataimakin ministan hukumar lafiya ta kasar Sin Wang Hesheng, ya gabatarwa taron wata sanarwa mai taken "Bunkasa matakan samar da lafiya: Cin gajiyar makoma da harkokin lafiya a nan gaba" a madadin rukunin kula da lafiya na hadin gwiwar tattalin arzikin Asiya da fasifik (APEC).

Wang ya bayyana cewa, a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, kasar Sin ta dade tana goyon bayan MDD, tare da shiga a dama da ita cikin ayyukanta na bunkasuwa. A cikin sama da rabin karni, kasar Sin ta tura likitoci da nas-nas dubu 26 zuwa kasashe da yankuna 71, inda suka warkar da marasa lafiya miliyan 280. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China