Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNECA ta bukaci kasashen Afrika su rungumi amfani da fasahar zamani don bunkasa masana'antu
2019-07-04 09:55:47        cri

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA) ta bukaci masu tsara dabarun ci gaba da 'yan kasuwa wajen ci gaba da yaki da talauci, kana su yi kokarin bunkasa fasaha ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zamani.

A cewar ECA, ko da yake yanayin da ake ciki na juyin juya halin harkokin masana'antu a kasashen Afrika yana tattare da kalubaloli, sai dai a hannu guda, wata muhimmiyar dama ce ta habaka ci gaban masana'atun da samar da tsarin yin gogayya a tsakaninsu, wanda ba za'a taba kaucewa hakan ba.

Ta kara da cewa, yarjejeniyar ciniki maras shinge a tsakanin kasashen nahiyar, wata dama ce ga gwamnatocin Afrika wajen kafa wani tsarin hadin gwiwa game da bunkasa tattalin arziki ta hanyar ci gaban zamani, da kuma samar da damammakin raya masana'antu ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani da kuma karfafa hulda a tsakanin 'yan kasuwar Afrika.

Game da muhimmancin yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afrika, hukumar ECA ta bayyana cewa, tana yin aiki tare da kungiyar tarayyar Afrika (AU) wajen bunkasa muhimmin tsari, ta yadda zai ba da damar kowane bangare ya amfana wajen samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar ci gaban zamani a tsakanin kasashen Afrika da shiyyoyi.

ECA ta yi wannan kira ne gabanin fara taron ministocin kudi da raya tattalin arziki na kasashen Afrika, wanda za'a gudanar a Addis Ababa na kasar Habasha, a wata mai zuwa game da makomar masana'antun Afrika da bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar ci gaban zamani.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China