Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya ba da umarnin kwashe 'yan kasar daga Afrika ta kudu
2019-09-10 09:32:28        cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin kwashe dukkan 'yan Nijeriya dake son komawa gida daga Afrika ta kudu, biyo bayan harin nuna kyama da ake kai wa baki dake zaune a kasar.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce matakin na shugaba Buhari, ya biyo bayan karbar rahoton manzon musammam da ya aike zuwa Afrika ta kudu, wanda ya je kasar don ya bayyana damuwar shugaban game da harin da ake kai wa 'yan Nijeriya da kadarori ko kasuwancinsu a kasar.

Muhammadu Buhari, ya jaddada bukatar gwamnatin Afrika ta Kudu ta dauke matakan dakile hare haren da ake kai wa baki 'yan kasashen Afrika.

Ya kuma ce a shirye kasarsa take, ta hada hannu da gwamnatin Afrika ta kudu, wajen samar da dauwamammiyar mafita ga matsalar aikata laifuka daga wasu 'yan Nijeriya tsiraru.

A kalla 'yan Nijeriya 640 ne ake sa ran za su koma gida daga Afrika ta kudu, biyo bayan hare-haren da ake kai wa baki a kasar.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China