Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira ga 'yan Najeriya da su kai zuciya nesa kan hare-haren wariyar launin fata da ake kaiwa 'yan kasar a Afirka ta kudu
2019-09-05 12:53:39        cri

Shugaban hukumar wayar da kan jama'a ta Najeriya, Garba Abari, ya yi kira ga 'yan kasar, da su kai zuciya nesa su kuma kasance masu martaba doka, duk da hare-haren nuna wariyar launin fata da ake kaiwa 'yan kasar dake zaune a kasar Afirka ta kudu.

Garba Abari, ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar wadda Xinhua ya samu kwafenta.

Ya ce, yanzu haka dai gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da gwamnatin Afirka ta kudu, kuma dukkan kasashen biyu na daukar matakan da suka wajaba don daidaita wannan lamari.

A ranar Talata ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tura wata tawaga ta musamman da ake sa ran za ta isa Afirka ta kudu a yau Alhamis, biyo bayan hare-haren da suka rutsa da 'yan Najeriya a kasar.

Shugaba Buhari ya bukaci tawagar, da ta nunawa takwaransa na Afirka ta kudu rashin jin dadinsa kan abin da ya faru, kana su tattauna da shi game da yanayin.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa, Najeriya na duba yiwuwar dawo da jakadanta dake Afirka ta kudu gida, a wani mataki na magance hare-haren nuna wariyar launin fata da ake kaiwa 'yan Najeriya a kasar.

Onyeama ya kuma tabbatar da cewa, Najeriya ta kaucewa, taron dandalin tattalin arziki na duniya (WEF) kan Afirka, da aka bude jiya Laraba a birnin Cape Town na Afirka ta kudu, don nuna adawa da yadda ake lalata dukiyoyi da wuraren kasuwancin 'yan kasarta dake Afirka ta kudu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China