Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala babban zauren MDD kaso na 73
2019-09-17 19:31:35        cri

A jiya Litinin ne aka kammala babban zauren MDD karo 73, inda

Shugabar zaman mai barin gado Maria Fernanda Espinosa Garces, ta mika ragamar zauren ga zababben shugaban sa na 74, Tijjani Muhammad-Bande.

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya gabatar da jawabin taya murnar kammala zaman zauren na 73. A cikin jawabin na sa, Guterres ya ce mafi yawan batutuwa da aka yi muhawara, da wadanda aka yi tsokaci a kan su, yayin zaman da ya gabata, sun shaida irin nasarorin da za a iya cimmawa, muddin an samu shugabanci na gari, an kuma yi hadin gwiwa tsakanin sassan kasashen duniya.

Ya ce amincewa da dokokin taron guda biyu, wato na batun bakin haure da 'yan gudun hijira, sun isa misali dake tabbatar da haka. Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata, majalissar ta ci gaba da daukar karin matakai, na gaggauta aiwatar da sauye sauye daga dukkanin fannoni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China