Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika na goyon bayan yarjejeniyar haramta gwajin makaman nukiliya
2019-09-10 13:46:37        cri

Kasashen Afrika sun sake jaddada matsayarsu dake mara baya ga yarjejeniyar haramta gwajin makaman nukiliya.

Zaunannen wakilin Uganda a MDD Adonia Ayebare ne ya bayyana haka, yayin taron zauren majalisar, kan ranar yaki da gwajin makaman nukiliya ta duniya, inda ya ce, a madadin kasasken Afrika, yana mai bayyana cewa, suna mara baya ga yarjejeniyar, wadda ke da nufin tabbatar da haramci kan gwaje-gwajen makaman nukiliya da abubuwan da suke haifarwa da kuma dakile yaduwar makaman.

Ya ce, nahiyar Afrika na daukar batun ba da gudunmuwa ga tabbatar da babu makaman nukiliya a fadin duniya da cimma burin kawar da su da dakile yaduwarsu da muhimmanci, lamarin da ya ce, zai kawo zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China