Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU da MDD sun gana kan yadda za a rika kula da kayayyakin aikin soja a Somaliya
2019-09-06 10:53:10        cri

'Yan sanda da dakarun kasashe dake aiki a karkashin laimar tawagar kungiyar tarayyar Afirka AU da MDD dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, a jiya Alhamis sun kammala taron kwanaki biyu da nufin tabbatar da cewa, ana kula da kayayyakin aikin dakarun yadda ya kamata.

Wata sanarwa da tawagar AU ta fitar, ta bayyana cewa, taron ya samu halartar jami'an sojojin AMISON daga kasashen Burundi da Kenya da Uganda, suna kuma samun kayan aiki ne daga abokan hulda na kasa da kasa.

Tawagar ta kuma bayyana damuwa game da yadda kayan aikin dakarun ke saurin lalacewa, saboda munin yanayin wurin da ake aiki da su.

A nasa jawabin, mataimakin kwamandan AMISON mai kula da ayyuka da tsare-tsare James Nakibus, ya bayyana cewa, suna fuskantar kalubale da dama wajen kula da irin wadannan kayan aiki.

Jami'an sojojin da suka halarci taron, sun kuma tattauna kalubale da suke fuskanta wajen gyara kayayyakin aikin da tawagogin na AMISON suke amfani da su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China