Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da mutuwar mutane 5 sanadiyyar rushewar gini a Nijeriya
2019-08-20 09:10:14        cri

Mutane 5 sun mutu, bayan wasu gidaje sun rushe a wurare 2 mabanbanta dake jihar Jigawa na arewa maso yammacin Nijeriya.

Shugaban yankin karamar hukumar Kirikasamma Salisu Garba-Kubayo, ya ce ifti'la'in ya auku a yankin ne biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki ana yi.

Jami'in ya shaidawa manema labarai cewa, mamakon ruwan saman ya haifar da ambaliya a kauyuka 30 na yankin karamar hukumar Kirikasamma, baya ga gidaje akalla 330 da suka lalace.

A ranar 7 ga watan nan ne hukumar tunkarar ambaliya ta kasar dake da alhakin yin gargadi kan aukuwar ambaliya, ta yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliya a kasar, saboda ruwan sama mai karfi a fadin kasar.

Hukumar ta yi hasashen a bana, dukkan jihohin kasar 36 da birnin tarayyar Abuja, za su fuskanci matakai daban-daban na ambaliya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China