Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Samun ci gaba mai dorewa shi ne burin kasar Sin
2019-09-15 15:55:37        cri

Zhang Yongjing, shehun malami a kwalejin nazarin harkokin al'umma da na kasa da kasa ta Jami'ar Ottawa ta kasar Canada, ya ce kasar Sin ta fitar da sama da mutane miliyan 700 daga kangin talauci cikin gomman shekarun da suka gabata, kuma al'ummar Sinawa sun mori ingantacciyar rayuwa, wadda ita ce gagarumar nasarar da kasar ta samu tun bayan kafuwar jamhuriyar al'ummar kasar Sin a shekarar 1949.

Yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, gabanin cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, Zhang Yongjing ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samu gagarumar nasara wajen takaita gurbatar yanayi, da samar da dazuka da yaki da hamada da kuma juya bola.

A cewar hukumar kiddidiga ta kasar Sin, a shekarar 2018, birane 121 daga cikin 338 sun samu ingantuwar iska, adadin da ya kai kaso 35.8 bisa dari, wanda ya karu da kaso 14.2 bisa dari a kan shekarar 2015.

Ya ce ba haka kawai aka samu ingantuwar yanayin ba, yana mai cewa, sakamako ne na irin lokaci da albarkatu da aka zuba da kuma kyakkyawan kudurin shugabanci, inda ya ce, samun ci gaba mai dorewa shi ne burin kasar Sin a nan gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China