![]() |
|
2019-09-10 09:36:39 cri |
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kakkausar suka kan rikicin da ya auku ranar Lahadi a birnin Johannesburg, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 2, yana mai bayyana shi a matsayin laifin dake adawa da ci gaban kasar.
Mutane 2 sun mutu, bayan wasu 'yan kungiyar masu dauke da makamai, sun harbe su tare da daba musu wuka, ranar Lahadi, a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin.
Da yake tsokaci, Cyril Ramaphosa ya yi kira ga hukumomin tsaro su kara tsauri wajen yaki da daukar doka a hannu.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci keta doka da tada rikicin da zai shafi tsaron rayukan miliyoyin 'yan kasar ba, da baki 'yan kasashen waje dake kiyaye dokoki, kuma suke da 'yancin gudanar da rayuwa da kasuwancinsu cikin lumana.
Shugaba Ramaphosa ya ce rikicin ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar. Yana mai cewa, lamarin na tarnaki ga dukkan kokarin da ake na samun ci gaban kasar Afrika ta kudu, mai ba da damarmaki ga dukkan mazaunanta. (Fa'iza Msutapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China