Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta cika alkawarinta na sauke nauyi yadda ya kamata
2019-09-09 13:59:20        cri

A 'yan shekaru da suka wuce, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi a fannonin goyon bayan ayyukan MDD na kiyaye zaman lafiya, da biyan lissafin kudaden ayyukan MDD da aka ware mata, kana tana kara taka muhimmiyar rawa wajen kara azama kan yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da kuma yaki da talauci a duniya, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin na sauke nauyin da aka dora mata a matsayin wata babbar kasa.

Kwanan baya, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya jinjina wa kasar Sin bisa gudummowar ta kan MDD a shekarun baya, inda ya ce, ana yaba wa kasar Sin kwarai da gaske, saboda yanzu ana kalubalantar ra'ayin kasancewar bangarori daban daban, amma Sin na tsayawa kan ra'ayin sosai, tare da kiyaye tsarin kasancewar bangarori daban daban. Wannan kasa da ke gabashin duniyarmu tana kara taka muhimmiyar rawa cikin tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, lamarin da ya yi amfani wajen kara kafa duniya mai adalci da jituwa.

Bisa tanade-tanaden da ke cikin takardar bayani da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar a watan Yulin bana dangane da harkokin tsaron kasa a sabon zamani, an ce, kasar Sin tana mara wa MDD baya sosai wajen kiyaye zaman lafiya a duniya, wadda ita ce daya daga cikin manyan kasashen da suka fi biyan kudin kiyaye zaman lafiya, kana kuma ta fi tura sojojinta cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, gwargwadon sauran kasashe masu kujerun din din din a kwamitin tsaro na MDD. Ya zuwa watan Disambar shekarar 2018, sojoji fiye da dubu 39 na kasar Sin sun shiga ayyuka 24 na MDD wajen kiyaye zaman lafiya a duniya, kana wasu 13 daga cikinsu sun rasa rayukansu a fagen yaki na tabbatar da tsaro a duniya.

Alkaluman kididdigar da MDD ta gabatar a watan Mayun bana sun nuna cewa, yanzu haka sojoji da 'yan sanda kimanin dubu 2 da dari 5 na kasar Sin ne suke kare zaman lafiya a wasu sassan duniya, ciki har da mata 70.

Har ila yau ya zuwa ranar 7 ga watan Mayun bana, a matsayinta na kasa ta biyu wajen biyan lissafin kudi na yau da kullum na MDD, kasar Sin ta riga ta biya lissafin kudin MDD da aka ware mata, da kuma sauran kudaden da suka wajaba duka. MDD ta ce, kasar Sin ta sauke nauyin da aka dora mata yadda ya kamata, tana tsayawa tsayin daka kan sha'anin MDD da ra'ayin kasancewar bangarori daban daban.

A watan Satumban shekarar 2015, kasar Sin ta sanar da kafa asusun taimakawa yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, tare da dalar Amurka biliyan 2 a mataki na farko. Sa'an nan a watan Mayun shekarar 2017, kasar Sin ta sanar da karin tallafin kudi har dalar Amurka biliyan 1. Asusun ya kasance wani asusun musamman na ba da kudin taimako, wanda gwamnatin Sin ta kafa domin goyon bayan sauran kasashe masu tasowa, wajen aiwatar da ajandar ayyuka na shekarar 2030 ta samun ci gaba mai dorewa.

Cikin shekaru 40 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, kasar Sin ta fitar da mutane fiye da miliyan 700 daga kangin talauci. Ta kuma ba da babbar gudummowa wajen yaki da talauci a duniya. Sakamakon kiran kasar Sin, da kuma kara azama da take yi, ya sa babban taron MDD karo na 73 ya zartas da daftarin shirin dokar "kau da talauci a yankunan karkara, a kokarin aiwatar da ajandar ayyukan shekarar 2030 ta samun ci gaba mai dorewa" a watan Disamban shekarar 2018, karo na farko ne babban taron MDD ya zartas da kuduri, dangane da kau da talauci a yankunan karkara a tarihinsa, a kokarin inganta hadin gwiwar kasa da kasa, da taimakawa bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa ta yankunan karkara da ke kasashe masu tasowa, da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama bisa tunanin yin hadin gwiwa domin amfanawa kowa.

Haka zalika, kasar Sin na nacewa kan mara bayan yarjejeniyar Paris, dangane da batun sauyin yanayi, tare da yin kira da a samu ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. A watan Satumban shekarar 2015 ne kasar Sin ta sanar da samar da kudin Sin RMB biliyan 20, wajen kafa asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan batun sauyin yanayi, domin taimaka wa kasashe masu tasowa wajen daidaita sauyin yanayi.

A matsayinta na kasar da ta shiga ayyukan kafa MDD, kuma wadda ke da kujerar din din din a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta shiga ayyukan daidaita batutuwan da ke jawo hankalin al'umma ta hanyar siyasa, tana kin yarda da danniya, da ra'ayin nuna bangaranci, da samar da daidaita batutuwa bisa ma'auni iri 2, tana kuma kara azama kan yin tattaunawa da aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD daga dukkan fannoni.

Yanzu kasar Sin da ke cika alkawarinta kullum, da sauke nauyinta yadda ya kamata, tana kara ba da taimako wajen samun zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China