Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayayyakin da jiragen kasan Xinjiang suke jigilarsu a bana za su kai ton miliyan 150
2019-09-10 10:24:21        cri

Kawo yanzu yawan kayayyakin da jiragen kasan jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, suka yi jigilarsu a bana, ya zarce ton miliyan 100.

Hukumomin kula da sufurin jiragen kasa na jihar, na sa ran yawan kayayyakin da za a yi jigilarsu ta jiragen kasa a bana, zai zarce ton miliyan 150.

Daga watan Janairu zuwa Agusta, jihar Xinjinag ce ta zo ta daya, a karuwar yawan kayayyakin da jiragen kasa suka yi jigilarsu a kasar Sin.

Mataimakin daraktan sashen jigilar da kayayyaki na kamfanin kula da jiragen kasa na China Railway Urumqi Group Gao Lei, ya ce a bana, sassan dake kula da bangaren na jihar Xinjiang, sun kara inganta sufurin jiragen kasa baki daya.

Sassan sun karfafa ginin kayayyakin da ake bukata na inganta ba da hidima, da fadada ayyukan manyan tasoshin dakon kayayyaki da inganta ayyukan dauka da sauke kayayyaki da kuma ingancin jigilarsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China