Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummun kasa da kasa sun yaba da bayanin gwamnatin Sin kan aikin horas da sana'a a Xinjiang
2019-08-19 20:13:26        cri

A ranar 16 ga wata ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da "aikin horas da sana'a a jihar Xinjiang", inda aka yi cikakken bayani kan yadda ake gudanar da aikin a jihar. Kan wannan batu, al'ummun kasashen duniya sun yaba da bayanin matuka, kuma suna ganin cewa, matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka zai taimaka wajen dakile ayyukan ta'addanci da tunanin masu tsatsauran ra'ayi, haka kuma zai samar dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar

Shugaban kungiyar hada kan Sin da Afirka ta kasar Morocco Nasser Bouchiba ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta kafa cibiyar horas da sana'a a jihar Xinjiang bisa doka, kuma ta dauki matakin ne domin dakile ayyukan ta'addanci, haka kuma zai magance aukuwar ayyukan ta'addanci yadda ya kamata.

Masanin harkokin kasa da kasa na kasar Kenya Edhurley Cavens yana mai cewa, horas da sana'a ga matasa zai samar musu da damammakin samun kwarewar sana'a da tunanin da ya dace a gare su, haka kuma zai ba su damammakin taka rawa ga ci gaban zaman takewar al'umma, kana mataki ne mai dorewa wajen dakile ayyukan ra'addanci da tunanin tsattsauren ra'ayi, ya dace kasashen Afirka su koyi wannan fasaha daga kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China