Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun kasashe 37 suna goyon bayan matsayin Sin kan jihar Xinjiang
2019-07-15 20:02:08        cri

A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a wurin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, jakadun kasashen duniya da yawansu ya kai 37, sun aike da wata wasika ga hukumar MDD mai lura da hakkin dan adam, bayan da suka sakaya sunayensu, inda suka nuna goyon bayansu ga matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun dake shafar jihar Xinjiang ta kasar, lamarin da ya ba da amsa ga wasu kasashen yamma, wadanda suka zargi kasar Sin kamar yadda suke so.

Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin tana sanya kokari tare da sauran kasashen duniya, wajen tabbatar da ka'idojin kiyaye hakkin dan adam na MDD, tare kuma da daidaita batutuwan dake shafar hakkin dan adam bisa adalci, ta hanyar gudanar da shawarwari da hadin gwiwa, ta yadda za a ciyar da aikin kiyaye hakkin dan adam gaba a duk fadin duniya.

Geng Shuang ya kara da cewa, yayin da jihar Xinjiang ta kasar Sin take fuskantar kalubalen ta'addanci da masu tsatsauren ra'ayi, ta dauki matakai a jere domin dakile su, har ma ta cimma burin tabbatar da yanayin tsaro a jihar cikin nasara, kuma abu mafi faranta rai shi ne, a cikin shekaru uku da suka gabata, ba a taba ganin aukuwar hargitsi a jihar ba, kana al'ummun jihar suna rayuwa cikin jin dadi da lumana. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China