Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan MDD daga kasashe 8 sun ziyarci yankin Xinjiang
2019-09-04 09:58:03        cri

Wata tawagar MDD daga kasashe 8, ta ziyarci yankin Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin daga ranar 28 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba, bisa gayyatar ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, don su ganewa idonsu, irin nasarorin da yankin ya samu daga shirin yaki da tsattsauran ra'ayi da kuma kawar da talauci.

A yayin da suka ziyarci Hotan da Kashgar, an nunawa jami'an diflomasiyar wani shiri na noman laimar kwadi don kawar da talauci da wasu masana'antun sarrafa karo da ake tafiyarwa a kauyuka da dama.

Wakilin dindindin na kasar Mozambique a ofishin MDD dake Geneva Amadeu Paulo Samuel da Conceicao, ya yi fatan za a gabatar da shirin yaki da talauci na kasar Sin a Afirka.

Jami'an sun kuma ziyarci cibiyoyin koyar da sana'o'i da samun horo a Hotan da Kashgar, inda suka tattauna da dalibai da malaman dake cibiyoyin. Daga bisani sun ziyarci iyalan daya daga cikin daliban da suka kammala shirin samun horo da koyon sana'o'in, inda suka ga yadda cibiyar ta taimakawa matashin da masu tsattsauran ra'ayin addini suka canja tunaninsa, kuma yanzu haka ya samu aikin yi, har ya kafa iyali mai cike da farin ciki.

A nasa jawabin, wakilin dindindin na kasar Yemen a ofishin MDD dake Geneva Ali Mohamed Saed Majawar, yabawa ya yi da damar kawo ziyayar da aka ba su, wadda a cewarsa, ta ba su damar fahimtar matakan kasar Sin na yaki da ayyukan ta'addanci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China