Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manoma dubu 11 za su amfana daga shirin bunkasa aikin gona a Nijeriya
2019-08-20 10:55:46        cri

Bisa labarin da muka samu daga shafin jaridar Leadership A Yau, shirin bunkasa aikin gona da rayuwar al'ummar kasa, ya sanar da cewa, manoma dubu goma sha daya ne za su amfana daga shirin a jihar Kaduna.

Dokta Yahaya Aminu, shugaban aiwatar da shirin ne ya bayyana hakan a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da shirin ya gudanar a Zariyan jihar Kaduna, don wayar da kan manoma da masu kananan masana'antu alfanunsa.

A cewar dokta Yahaya Aminu, sana'ar noma tana taimaka wa rayuwa da zamantakewar jama'a, inda ya ce, harkar noma na kawar da kwadayi da zaman kashe wando, musamman a tsakanin matasa, tare da samar da hanyoyi masu yawa da manomi zai samu kudin shiga da kuma samar da dogaro da kai a tsakanin al'umma.

A cewar sa, ana aiwatar da shirin ne kan masara da citta da kuma samar da madara ta hanyar kiwon shanu.

Shugaban ya kuma kara da cewa, manoma dubu sha daya ne za su amfana karkashin shirin na shekaru biyar, kamar yadda tsarin ya tanadar. (Leadership A Yau, Fa'iza)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China