Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta samu nasara kan Sin a gasar kwallon kwando ta hukumar FIBA
2019-09-09 09:14:35        cri

Kungiyar kwallon Kwando ta Najeriya, ta samu nasara kan takwarar ta ta kasar Sin da maki 86 da 73, a gasar kasa da kasa da ke gudana yanzu haka wadda hukumar FIBA ke shiryawa. Nasarar da Najeriyar ta samu dai ya ba ta gurbi a gasar Olympics da za ta gudana a birnin Tokyo daga rukunin M.

Bayan da Iran ta doke Philippines da maki 95 da 75 daga rukunin N, yanzu haka Sin ta rasa damar samun gurbi a gasar ta Tokyo kai tsaye a gasar jiya.

Da yake tsokaci game da rawar da ya taka yayin wasannin da Sin ta buga, 'dan wasan Sin da ke kan gaba wajen samun maki a gasar Yi Jianlian, ya ce, "Wasannin sun yi zafi matuka, na yi kokarin ganin mun yi nasara a wasannin karshe da zan buga a wannan sana'a tawa".

A nasa bangare, mai horas da 'yan wasa daga tawagar Najeriya Alexander Nwora, ya ce, "Ina alfahari da 'yan wasa na. Sin na da 'yan wasa kwararru, ga kuma magoya baya masu yawa. Amma duk lokacin da 'yan wasan na Sin suka yi kokarin cike gibin wasan, 'yan wasa na suna kara kaimi."

Azagaye na 4 na wasan, Najeriya ta yi gaba da maki 60 da 51. Amma minti 7 kafin karshen wasan, Yi Jianlian ya rage gibin makin wasan zuwa 62 da 59. Ya zuwa mintuna 2 kafin tashi daga wasan, Najeriya ta kara yawan kwallaye zuwa maki 80 da 71.

Bisa jimillar yawan maki da 'yan wasan kungiyoyin biyu suka samu, Okogie daga Najeriya na da maki 16, yayin da Yi Jianlian daga tawagar Sin ke da maki 27.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China