Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta yi nasara a karon farko a gasar FIBA
2019-09-05 09:31:32        cri
Kungiyar kwallon kwando ta Najeriya ta doke takwararta ta kasar Koriya ta kudu da maki 108 da 66, a wasan ranar Larabar nan da suka buga, yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya na hukumar FIBA na bana.

To sai dai kuma duk da nasarar da ta samu, kungiyar ta Najeriya ba ta samu gurbin buga zagaye na biyu na kungiyoyi 16, dake fafatawa a gasar ba daga rukunin B. Hakan kuwa ya biyo bayan rashin nasara da ta yi a wasannin ta guda biyu a jere kafin wasan na Laraba.

Yanzu dai Najeriya da Koriya ta kudu za su tafi birnin Guangzhou, domin buga wasan karkare gasar daga ranar Asabar mai zuwa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China