Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bloomberg: Sin da Indiya za su zama manyan cibiyoyin fasaha na duniya nan da shekarar 2035
2019-07-25 10:52:45        cri

Sama da rabin adadin kwararrun masana harkokin kasuwanci na kasa da kasa da suka shiga wani bincike na Bloomberg sun amince cewa, an yi hasashen nan da shekarar 2035 kasashen Sin da Indiya za su kasance manyan cibiyoyin fasahohin zamani na duniya.

Kusan kashi 60 bisa 100 da suka fito daga kasashe masu tasowa da kusa kashi 49 bisa 100 wadanda suka fito ne daga kasashe masu ci gaba sun bayyana cewa kasashen Sin da Indiya za su iya kasancewa a matsayin manyan cibiyoyin fasahohin zamani na duniya nan da wasu gomman shekaru masu zuwa, kamar yadda alkaluman sabon bincike da taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na Bloomberg suka gudanar kan kwararrun 'yan kasuwa sama da 2,000 daga kasuwanni guda 20 suka bayyana.

Binciken yana daga cikin taron dandalin tattaunawar tattalin arziki na Bloomberg a wannan shekara wanda za a gudanar a Beijing, a ranar 20 zuwa 22 ga watan Nuwamban bana. Kusan manyan kwararrun masana kasuwanci na kasa da kasa 500 na kasashe da shiyyoyin duniya sama da 60, ciki hadda wakilan gwamnatoci, da masana daga jami'o'i ne za su shiga dandalin na bana. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China