Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Sin da suka shahara sun fi mayar da hankali kan fasahar AI
2019-09-06 09:14:44        cri

Wani rahoton bincike da aka fitar ya nuna cewa, yanzu haka kamfanonin kasar Sin da suka shahara, sun fi mayar hankali kan raya fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam(AI).

Rahoton ya ce, kamfanonin kasar Sin 11 cikin 25 da shafin Linkedln na kasa da kasa ya ayyana a matsayin mafiya shahara, sun sanya fasahar AI a kan gaba cikin harkokinsu na kasuwanci, tare da hade manhajojin kamfanonin da ragowar fasahohin kere-kere na yau da kullum waje guda, Kamar yadda kamfanin ya bayyana cikin rahoton, bayan kaddamar da jerin sunayen kamfanonin kasar da suka shahara.

Wadannan kamfanoni dai sun mayar da hankali wajen kera, masarrafar kwanfuta, da fasahar kirkire-kirkire, da na'urorin lafiya na zamani, da birane na zamani, da fasahohin cinikayya na zamani, da na'urorin harhada magunguna na zamani da sauran fannoni.

Rahoton ya kara da cewa, tasirin fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam kusan ya karade dukkan masana'antu, lamarin da ya zama ruwan dare ga duniya. Adadin shekarun ma'aikatan da ke aiki a irin wadannan kamfanoni da suka shahara, bai wuce shekaru 28 ba, kuma kaso 10 cikin 100 na wadannan ma'aikatan sun yi karatu ko aiki a ketare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China