Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahotoļ¼šJami'o'in kasar Sin na taimakawa bangaren kwaikwayon tunanin dan-Adam
2019-05-20 13:53:59        cri
Wani rahoto da cibiyar raya sabbin dabarun kwaikwayon tunanin dan-Adan ta kasar Sin (CINGAI) ta fitar, ya bayyana cewa, jami'o'in kasar, sun ba da gagarumar gudummawa kan yadda kasar take raya sashen kwaikwayon tunanin dan-Adam.

Rahoton wanda aka wallafa a ranar Asabar din da ta gabata, ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2019 da muke ciki, jami'o'in kasar Sin 94 sun kafa makarantu ko cibiyoyin binciken tunanin dan-Adam kuma 40 daga cikinsu an kaddamar da su ne a shekarar 2018 da ta gabata. Kuma a cikin shekarar ta 2018, dukkansu sun wallafa takadu 19,374 game da nazarin tunanin dan-Adam. Adadin da ya dara na kasar Amurka.

Bugu da kari, akwai cibiyoyin bincke 75 a sassan kasar wadanda ke gudanar da bincike game da nazarin tunanin dan-Adam, raya fasahar kere-kere da zakulo masu basira. Kamar yadda wani rahoton da aka gabatar a taron fasahar tunanin dan-Adam na duniya karo na uku da ya gudana a birnin Tianjin dake yankin arewacin kasar Sin ya bayyana.

Da yake karin haske, masanin tattalin arziki a cibiyar ta CINGAI Liu Gang ya bayyana cewa, masanan kasar Sin suna kokarin bullo da matakan kirkire-kirkire da za su raya bangaren raya fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam.

Daga cikin masana'antun dake raya tunanin dan-Adam na kasar Sin 745, kaso 75.2 cikin 100 suke amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin dan-Adam. Yayin da kaso 2.8 cikin 100 kawai suke nazarin ilimin da ya shafi kwaikwayon tunanin dan-Adam, sai kaso 22 cikin 100 dake gudanar da bincike kan fasahar kere-kere.

A bangaren amfani da manhaja kuwa, akwai masana'antu 18 dabam-dabam ciki har da masu kere manhajoji kan tunanin dan-Adam, da fashohin harkokin kudi, kafofin yada labarai na zamani da sabbin na'urorin cinikayya da na tsaro kan fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China