Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin Amurka ba su so su bar babban kamfanin kera kayayyakin Sin
2019-08-28 19:28:58        cri

Yau Laraba gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya fitar da wani sharhi mai taken "Kamfanonin kasar Amurka ba su so su bar kasar Sin, babban kamfanin kera kayayyaki na duniya", inda aka yi nuni da cewa, a farkon watanni shida na bana, adadin jarin da kamfanonin kasar Amurka suka zuba a kasar Sin ya kai dala biliyan 6 da miliyan 800, adadin da ya karu da kaso 1.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekaru biyu da suka gabata, alal misali, kamfanin Tesla dake kera motoci masu amfani da wutar lantarki ya kafa reshensa a birnin Shanghai na kasar Sin, kana asusun Bain Capital na Amurka ya zuba jarin da yawansa ya kai dala miliyan 570 a cibiyar samar da bayanai ta Chindata ta kasar Sin, wadannan manyan kamfanonin Amurka sun shaida ta hanyar daukar hakikanan matakai cewa, ba su so su bar kasuwar kasar Sin, har ma za su kara zuba jari a kasuwar ta kasar Sin.

Sharhin ya bayyana cewa, babu wani kamfani da zai kau da kai ga babbar kasuwar kasar Sin wadda ke da masu sayayya da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400, kana a matsayinta na kasa daya kacal wadda take da daukacin nau'o'in masana'antun da MDD ta tsara, kasar Sin tana iya samar wa manyan kamfanonin kasa da kasa cikakken rukunin masana'antu da cikakken rukunin samar da kayayyaki, a don haka kamfanonin kasa da kasa suna samun rangwame na kudin da suka kashe a kasar Sin, wannan shi ma babban fiffiko ne na kasar Sin, kuma babu wata kasa za ta iya maye gurbinta.

Sharhin ya jaddada cewa, an dade da kafa irin wannan babban kamfanin kera kayayyaki na kasar Sin, kuma ba zai yiyu ba a kafa irinsa a wata kasa a cikin gajeren lokaci ba, shi ya sa matakin da Amurka ta dauka ya sabawa tsarin kasuwa, haka kuma ya lalata gudanarwar harkokin kamfanoni a fadin duniya, yanzu haka kasar Sin tana kara bude kofarta ga kasashen ketare, babban kamfanin kera kayayyakin kasar Sin zai kara habaka sannu a hankali, ko shakka babu kasar Sin za ta samar da karin damammakin kasuwanci ga daukacin kamfanoni masu jarin waje wadanda suke darajanta kasuwar kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China