Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsanantar takaddamar ciniki ba za ta daidaita matsala ba
2019-08-30 19:51:17        cri

Kwanakin baya wasu Amurkawa sun sanar da cewa, Amurka za ta sake kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin a matakai daban daban, lamarin da ya kara tsananta takaddamar cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka, hakika Amurka ba ta dauki matakin a hankali ba, a don haka ba zai daidaita matsalar dake tsakanin sassan biyu ba, haka kuma zai gurgunta muradun kasashen biyu, da ma na daukacin al'ummun kasashen duniya baki daya.

A cikin shekara guda da ta gabata, kasar Sin ta mayar da martani a hankali kan matakan matsin lamba da Amurka ta dauka har sau uku, domin kare muradunta, amma yanzu yakin cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka ya kara tsanani, har ya haifar da mummunan tasiri ga sassan biyu da kuma duniya baki daya, a irin wannan yanayi, kasar Sin tana ganin cewa, yanzu ya dace a kawo karshen matakin da Amurka ta dauka game da kara sanya haraji kan kayayyakin kasarta wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 550, saboda hakan zai sassauta yakin cinikayyar.

A matsayinsu na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, kasar Sin da Amurka suna da moriya iri guda, shi ya sa gudanar da hadin kai a tsakaninsu shi ne zabi mafi dacewa a gare su, kuma ya dace su daidaita matsalar ta hanyar yin tattaunawa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan matsayin adawa da tsanantar yakin cinikayya, har kullum tana son daidaita matsala sannu a hankali ta hanyar yin tattaunawa da hadin gwiwa, tana kuma fatan sauran Amurkawa ma za su kwantar da hankalinsu su daidaita matsalar a hankali, tare da kasar Sin bisa tushen daidaito da mutunta juna.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China