Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta dakile tasirin da takaddamar ciniki ta haifar mata
2019-08-29 19:38:31        cri

Yau gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Kasar Sin za ta dakile tasirin da takaddamar cinikayya ta haifar mata", inda aka bayyana cewa, kasar Sin ba za ta canja matsayinta na kiyaye muradun kasarta da na al'ummunta ba, kana za ta dakile tasirin da takaddamar cinikayya ta haifar mata. Wasu Amurkawa suna matsa lamba ga kasar Sin ta hanyar daukar matakin kara sanya haraji, amma hakarsu ba za ta cimma ruwa ba, saboda matakan da suka dauka ba su dace da hakikanin yanayin da ake ciki ba, sannan ba su fahimci saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ba, wasu kuma suna ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya shiga mawuyacin hali.

Sharhin ya jaddada cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da babban karfin a asirce, wannan shi ne dalilin da ya sa kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan mayar da martani ga cin zarafin cinikayyar da Amurka ta ke mata, yanzu haka kasar Sin tana kokarin dakile tasirin da takaddamar cinikayya take haifar mata ta hanyar kara habaka bukatun cikin gida da na kasuwarta, kana kasar Sin tana kara yiwa tattalin azrikin kasar gyaran fuska da kuma kara bude kofa ga kasashen ketare, duk wadannan matakai suna kara bunkasa tattalin arzikin kasar mai inganci gaba yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China