Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike da sakon taya murna ga bikin baje kolin Sin da kasashen Larabawa karo na 4
2019-09-05 14:25:47        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar bikin baje kolin kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 4 wanda aka bude a yau a yankin Ningxia mai cin gashin kansa na kabilar Hui dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana a cikin wasikar cewa, biyo bayan bukatun da ake da su na raya kasa, a 'yan shekarun baya bayan nan kasar Sin da kasashen Larabawa sun yi hadin gwiwa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya domin samun kyakkyawan sakamako.

A lokacin taron kolin hadin gwiwa na ministocin Sin da kasashen Larabawa wanda aka gudanar a Beijing a watan Yulin shekarar bara, bangarorin biyu sun amince za su gina muhimmiyar dangantaka ta matsayin koli mai kyakkyawar makoma a nan gaba, da nufin cimma nasarorin bunkasa ci gaban sassan biyu.

Bikin baje kolin na Sin da kasashen Larabawa karo na 4 zai samar da wani muhimmin dandali wanda zai amfanawa bangarorin biyu, da nufin samun damar zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, kana da ingiza hanyoyin samun bunkasuwarsu karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China