Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin sadarwa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya
2019-09-04 19:38:31        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci hukumar dake lura da harkokin dab'i da harsunan waje, da ta kara inganta ayyukanta na sadarwa, ta yadda hakan zai ba da damar gabatarwa duniya ainihin yanayin Sin a sabon zamani da ake ciki.

Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya yi wannan kira ne cikin sakon taya murna da ya aikewa hukumar, na cikar ta shekaru 70 da kafuwa.

Cikin wasikar, shugaba Xi ya mika sakon jinjina ga jami'ai, da ma'aikatan hukumar, da ma sauran baki 'yan kasashen waje dake aiki a hukumar da sauran aminai, wadanda ke tallafawa ayyukan Sin na sadarwa tsakaninta da sauran sassan kasa da kasa.

Da yake karin haske game da muhimmancin rawar da ta taka, wajen gabatarwa sassan kasa da kasa irin ci gaban da Sin ta samu, da shigar kasar fannonin musaya na kasa da kasa cikin shekaru 70 da suka gabata, Xi ya ce hukumar ta taka rawar gani, wajen bayyana labarun Sin da muryoyin ta, ga daukacin bangarorin duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China