Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya halarci bikin bude gasar kwallon kwando ta duniya ta bana
2019-08-31 15:49:07        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude qasar kwallon kwando ta duniya (FIBA) ta bana, jiya Juma'a a babban dakin wasan motsa jiki na Water Cube, dake nan birnin Beijing.

A jawabinsa na bude qasar, shugaban hukumar FIBA Horacio Muratore, ya ce qasar ta bana ita ce mafi girma, wadda kuma za a fi kallo a tarihin qasar kwallon kwando na duniya, kuma za a gudanar da ita birane mafi yawa.

Ya kuma jinjinawa shirye-shiryen da kasar Sin ta yi domin qasar, yana mai cewa, ya yi ammana qasar za ta cimma gagarumar nasara.

Tun da farko kafin bude qasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar ta FIBA, da yammacin jiya, inda ya jaddada cewa, tun bayan kafuwar Jamhuriyar al'ummar kasar Sin shekaru 70 da suka gabata, kokarin kasar a bangaren raya wasanni ya samu dimbin nasarori.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin, na gina kanta a kokarin zama jagora a fannin wasanni, kuma a shirye take ta hada hannu da hukumar FIBA wajen rayawa da yayata wasan kwallon kwando a kasar.

A nasa bangaren, Horacio Muratore ya ce FIBA na ba da muhimmanci sosai ga hadin gwiwarta da Sin, kuma ta shiryawa ba da gudunmuwa ga burin raya kwallon Kkwando a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China