Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar CAS ta Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da takwararta ta kasar Kenya
2019-09-03 09:51:59        cri
Cibiyar binciken kimiyya ta kasar Sin ko CAS a takaice, ta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da takwararta ta kasar Kenya ko AAS a takaice. An dai yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Litinin a birnin Nairobi, inda jagoran cibiyar CAS Bai Chunli, ya wakilci tsagin kasar Sin.

Ana dai fatan matakin zai ba da damar bunkasa harkokin bincike, da samar da ci gaba, da karfafa fasahohin zamani.

Da yake bayani game da wannan batu, Mr. Bai ya ce cibiyar CAS na martaba alakarta da kasashen nahiyar Afirka. Ya ce sanya hannu kan takardar yarjejeniyar, wani mataki ne mai muhimmanci a fannin inganta alaka tsakanin CAS da sauran cibiyoyin bincike na nahiyar Afirka. A nan gaba kuma, cibiyar na fatan fadada ayyukan hadin gwiwa da cibiyar AAS ta Kenya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China