![]() |
|
2019-09-04 15:51:38 cri |
Alkaluman kididdigar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, baki daya, kwatankwacin kudin da kasar Sin ta samu daga cinikin hidima ya kai yuan triliyan 3.09, wato dala biliyan 436 a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan ta 2019, inda ya karu da kashi 3.2% idan an kwatanta da makamancin lokacin bara.
Sabanin harkokin cinikayyar hajoji, cinikin hidima ya shafi sufuri da sadarwa da yawon shakatawa, gine gine, tallace tallace da sauransu.
Kasar Sin ta dauki kwararan matakan inganta cinikin hidima, wadanda ke kunshe da bude kofa a fannin hada-hadar kudi, ilmi, al'adu, da fannin kiwon lafiya.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China