Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da sabon yankin cinikayya maras shinge na gwaji a lardin Guangxi
2019-08-30 20:42:53        cri

A yau da safe ne aka kaddamar da sabon yankin cinikayya maras shinge na gwaji a jihar Guangxi ta kasar Sin, a wani mataki na kara yin gyare-gyare da bude kofa.

Jihar Guangxi mai cin gashin kanta ta kabilar Zhuang dake kudancin kasar Sin, ta gudanar da bikin kaddamar da yankin cinikayya maras shinge na gwaji ne a Nanning, babban birnin jihar. Manufar yankin gwajin na Guangxi, shi ne kokarin kulla alaka da yankin ASEAN. Fadin yankin cinikayya maras shinge na gwaji na Guangzi ya kai muraba'in kilomita 120.

A cewar gwamnatin jihar, yankin zai mayar da hankali kan hidimomin kudi na zamani, da tsare-tsare da cinikayya da ma masana'antun samar da kayayyaki masu tasowa, tsare-tsaren jigilar kayayyaki a tashohin ruwa, cinikayyar kasa da kasa, kayayyakin gyara na sabbin ababan hawa masu amfani da sabon makamashi, yawon shakatawa tsakanin kasashe.

Wata taswira da majalisar gudanar kasar Sin ta fitar a ranar Litinin, na nuna cewa, za a kafa sabbin yankunan cinikayya maras shinge na gwajin ne a lardunan Shandong, da Jiangsu, da Guangxi, Hebei, Yunnan da Heilongjiang, adadin yankunan na FTZ na kasar da ya kai 18. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China