Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta fitar da takardar bayani game da tsaron nukiliya
2019-09-03 10:42:56        cri

A yau ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani kan matakan da kasar ta ke dauka game da tsaron nukiliya.

Takardar mai taken "yadda kasar Sin ta ke tsaron nukiliya" ta yi bayani dalla-dalla kan ka'idoji da manufofin kasar a wannan fanni, da yadda za ta yi musayar matakan da ma yadda take aiwatar da ka'idojin tsaron nukiliyar, da fayyace kudurinta na tabbatar da tsaron nukiliya a duniya da matakan da ta dauka don cimma wannan manufa.

Takardar bayanin ta kuma bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, bangaren nukiliyar kasar, ya bunkasa cikin sauri, ya tsara sannu a hankali tare da kafa cikakken tsari, inda ya ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da tsaron makamashi, da kare muhalli, da inganta rayuwar jama'a, da raya ci gaban tattalin arziki mai inganci.

A matsayinta na kasar da ke kan gaba wajen yayatawa, da bunkasa da kokarin ganin an ci gajiyar tsarin tsaron nukiliya na duniya daidai wa daida, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron nukiliyarta, da cika ka'idoji na kasa da kasa da bunkasa alakar bangarori daban-daban kan tsaron nukiliya.

Takardar ta kuma karkare da cewa, kasar Sin ta jaddada bukatar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana don amfanin daukacin bil-Adama, ta kuma ba da tallafin kwarewa da karfinta ga tsarin tafiyar da tsaron nukiliya na duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China