Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gina kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama a fannin tsaron nukiliya
2019-09-03 15:19:55        cri

Wata takardar bayani da kasar Sin ta fitar Talatar nan, ta bayyana cewa, kasar tana fatan kafa tsarin tsaron nukiliya na kasa da kasa mai kunshe da shigogin nuna daidaito, da hadin gwiwa da cin moriyar juna, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan tafiyar da tsaron nulkiya ta hanyar daidaito da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da yin aiki da sauran kasashen duniya wajen gina kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama a fannin tsaron nukiliya.

Takardar mai taken "yadda kasar Sin ta ke tsaron nukiliya" ta kuma bayyana cewa, kasar Sin ta sauke nauyin kasa da kasa da kudurori na siyasa dake bisa wuyanta, da karfafa alaka tsakanin bangarori daba-daban a kokarin tabbatar da tsaron nukiliya da karfafa musaya da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya kan tsaron nukiliya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China