Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta yaba da hadin gwiwarta da Sin a fannin ilimin gaba da sakandare
2019-08-15 10:20:37        cri

Sakatare janar na ma'aikatar ilimi ta Kamaru, Wilfred Gabsa Nyongbet, ya yabawa kyakkywar dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin a bangaren ilimin gaba da sakandare.

Wilfred Nyongbet, ya bayyana haka ne a jiya, yayin bikin ban kwana da dalibai 128 na kasar, wadanda suka samu tallafin karatu daga kasar Sin, yana mai cewa, wannan ya nuna kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, daliban za su koyon irin fasahar da ake bukata domin ci gabn Kamaru, sannan a shirye suke, su ci gaba da hadin gwiwa a bangaren ilimin gaba da sakandare.

Daga cikin daliban 128, 45 sun ci gajiyar tallafi daga gwamnatin kasar Sin, yayin da 83 suka samu tallafi daga kwalejin Confucius.

Da yake jawabi, jakadan kasar Sin a Kamaru, Wang Yingwu, ya ce adadin tallafin karatu da kasar Sin ta ba daliban Kamaru a bana, shi ne mafi yawa tun bayan shekarar 2006. Ya kara da cewa, a shirye Sin take, ta hada hannu da Kamaru domin inganta hadin gwiwarsu a fannin ilimi zuwa wani sabon mataki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China