Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gudanar da taron gamayyar bangarorin kyautata yanayin halittu karo na 15
2019-09-04 10:55:44        cri

Kasar Sin za ta shirya babban taron gamayyar bangarori masu ruwa da tsaki wajen kyautata yanayin halittu karo na 15 wato COP15) a takaice, take taron shi ne, "Gina ingantaccen tsarin yanayin halittu don samar da makoma mai kyau ga dukkan halittun duniya" a shekarar 2020.

Taron, wanda zai gudana a Kunming, babban birnin lardin Yunnan dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Sin, zai sake bibiyar tsarin jadawalin shirin kiyaye halittu na shekarar 2020, kana zai yi nazari game da gabatar da sabbin tsare tsaren kyautata yanayin halittu nan da shekarar 2030.

Shugaban ma'aikatar muhalli da gandun daji na kasar Sin Li Ganjie ya ce, manufar taron tana da matukar muhimmanci wajen cimma nasarar samar da dawwamamman ci gaban yanayin halittu da kuma samun moriyar bai daya, ya bayyana hakan yayin da ya gabatar da sanarwar taron ga Cristiana Pasca-Palmer, babban sakataren hukumar kula da yarjejeniyar kiyaye yanayin halittu.

Li ya ce, kasar Sin za ta yi bakin kokarinta wajen sauke nauyin dake bisa wuyanta na shiryawa da karbar bakuncin taron don tabbatar da ganin an kammala taron mai cike da tarihi cikin nasara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China