Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta zuba yuan biliyan 13 ga ayyukan yaki da talauci
2019-05-24 09:36:50        cri

Jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, mai yancin cin gashin kanta, ta zuba kusan yuan biliyan 13.2, kwatankwacin dala biliyan 2, ga ayyukan yaki da talauci.

Ofishin dake kula da aikin yaki da talauci da samar da ci gaba a jihar, ya ce tsakanin watan Disamban bara da Afrilun bana, jihar ta ware yuan biliyan 13.2 ga asusu na musammam domin ayyukan rage fatara, adadin da ya karu zuwa kaso 81.7 bisa dari a kan na shekarun baya.

Kakakin ofishin Chen Lei, ya ce ya zuwa karshen watan Afrilun bana, manyan yankuna 4 na kudancin Xinjiang sun kaddamar da ayyuka kusan 1,900, daga cikinsu har da 1,387 da aka kaddamar a kananan yankuna 22 masu fama da matsanancin talauci, kuma ana sa ran kammala galibinsu tsakanin watan Satumba da Oktoba, inda mazauna yankunan za su ci gajiyar ayyukan a bana.

Domin karfafawa kwarin gwiwar jami'ai da mazauna shiga ayyukan yaki da talauci, an samar da jerin horo da za su mayar da hankali kan fahimtar dabarun yaki da talauci da aiwatar da su. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China