Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya aike da sakon taya murna ga taron baje kolin kayayyakin fasaha na 2019 na kasar Sin
2019-08-26 14:11:50        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron baje kolin kayayyakin fasaha da aka bude yau Litinin a birnin Chongqing na kudu maso yammacin kasar.

Cikin wasikar, Xi Jinping ya ce, a yanzu, fasahar sadarwa ta zamani da intanet da manyan bayanai da kwaikwayon tunanin dan Adam, na sauyawa cikin sauri.

Ya ce babban ci gaban da aka samu a wani sabon zagaye na yujin juya halin kimiyya da fasaha, da sauyin ayyukan masana'antu, da ci gaban da ake samu na fasahar zamani, sun haifar da kyakkywan tasiri kan bunkasar tattalin arziki da kyautata zamantakewa da shugabanci a duniya.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta mayar da hankali sosai kan ci gaban fasahar zamani da kara ingiza zamanintar da ayyukan masana'antu da tattalin arziki.

Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta yi aiki da al'ummomin kasa da kasa wajen samar da zamanin amfani fasahohi da musayar nasararorin da aka samu a bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China