Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci mambobinta su rika shiryawa gudanar sahihin zabe cikin nasara a Afrika
2019-08-31 15:40:10        cri

Tarayyar Afrika AU, ta bukaci kasashe mambobinta su rika shiri sosai tare da daukar managartan matakan gudanar da tsarin zabe cikin nasara da kuma magance duk wani rikicin bayan zabe da za a iya samu.

Yayin zamansa na baya bayan nan, kwamitin sulhu na tarayyar mai mambobi 55, ya tattauna kan zabukan nahiyar, tsakanin watan Junairu zuwa Disamban bana, inda kwamitin ya saurari rahotanni game da zabukan da aka yi a kasashen Nijeriya da Benin da Guinea Bissau da Mauritania da Senegal da Afrika ta kudu da sauransu.

Da yake jaddada muhimmancin shugabanci da kula da harkokin zabe, kwamitin ya karafafawa mamabobin tarayyar gwiwar tattara kudaden da ake bukata daga ciki da wajen nahiyar, domin taimakawa shirye shiryen zabe da inganta kwarewar hukumomin dake shirya zabukan.

Ya kuma yi kira da su shirya amfani da dukkan abubuwan dake akwai domin magance duk wasu batutuwa da za su iya yin mummunan tasiri a kan shirya zabuka a nahiyar, ciki har da lokutan zabe da kuma sauran wasu abubuwa da ka iya tarnaki ga zabukan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China