Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta taya sabon firaministan Sudan murna
2019-08-20 09:37:10        cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya taya Abdallah Hamdock murnar zama sabon firaministan kasar Sudan.

Mahamat ya kuma jinjinawa daukacin 'yan siyasa, da fararen hula, da ma sojojin kasar, bisa jajircewar su wajen tabbatar da nasarar sulhu, da sanya lamurran kasar gaban komai.

Ya ce, akwai bukatar ganin mahukuntan Sudan, tare da sauran masu rajin samar da sauye sauye a kasar, da masu dauke da makamai, sun hada karfi da karfe wajen ganin an cimma matsaya daya, cikin watanni shiddan farko na fara aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya, don tabbatar da samuwar cikakken yanayi na zaman lafiya da sulhu, wanda zai haifar da mika mulki ga zababbiyar gwamnati cikin lumana.

Daga nan sai ya jaddada aniyar kungiyar AU, ta ci gaba da mara baya ga al'ummar Sudan, a kokarin su na kaiwa ga kafa gwamnatin farar hula wadda kowa zai amince da ita.

An nada Abdallah Hamdock matsayin firaministan gwamnatin rikon kwaryar Sudan ne a ranar Lahadi, bayan sanya hannu kan dokar da ta tabbatar da tsarin mulkin kasar, wanda ya ba damar aiwatar da yarjejeniyar gudanar da gwamnatin hadaka, tsakanin sojoji da gamayyar 'yan adawa fararen hula dake kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China