![]() |
|
2019-08-30 15:03:24 cri |
Yayin bikin kaddamar da rundunar a fadar WhiteHouse, shugaban Amurka Donald Trump wanda ke tare da kwamandan rundunar na farko, John Raymond, ya ce wannan muhimmiyar rana ce, wadda ta mayar da hankali ga tabbatar da tsaro da kare sararin samaniyar Amurka.
Shugaba Trump ne ya bada umarnin kafa rundunar a karshen bara, inda ta zama hadakar rundunar tsaro ta 11 dake karkashin ma'aikatar tsaron kasar.
An yi ammana kafa sabuwar rundunar wani yunkuri ne na samar da rundunar tsaron sararin samaniya mai zaman kanta, shirin da har yanzu ke bukatar amincewar majalisar wakilan kasar. (Fa'iza Msuatpha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China