Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararre: Kara buga hajari kan kayayyakin kasar Sin zai sanya Amurka tafka hasara
2019-08-12 11:14:49        cri
Wani masani ya bayyana cewa, matakin Amurka na kara buga harajin kwastam kan kayayyakin da kasar Sin ke samarwa zai iya jefa masu samar da kayayyaki a kasar Amurka su tafka hasara, kana matakin zai iya haifar da koma-baya ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Eric Mangunyi, wani manazarci a jami'ar Walter Sisulu dake kasar Afrika ta kudu ya ce, buga harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin wadanda ake amfani da su wajen sarrafa wasu kayayyaki a kasar Amurka zai haifar da tafiyar hawainiya ga bunkasuwar tattalin arzikin Amurka saboda zai rage yawan adadin kayayyakin da ake samarwa.

A cewar Mangunyi, 'yan kasuwar Amurka tuni sun riga sun dandana kudarsu. Ya ce akwai yiwuwar kasar za ta iya samun koma-baya ta fuskar zuba jari a wasu fannoni da dama na tattalin arzikinta wadanda galibi sun ta'allaka ne kan irin kayayyakin da ake shigo da su zuwa kasar daga ketare.

Bugu da kari, Mangunyi ya bayyana cewa, a duniya baki daya, yawan zuba jari a kasashen duniya zai iya samun koma-baya, kuma hakan zai iya girgiza harkokin cinikayyar duniya. Ya ce baki daya wannan al'amari zai iya haifar da mummunan sakamako ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen duniya da ma ita kanta duniyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China