Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban kasar Saliyo 116 sun samu tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin
2019-08-30 10:17:57        cri
Ofishin jakadancin Sin dake Saliyo, ya bada tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin ga dalibai 116 na kasar, domin taimaka musu kara ilimi a kasar Sin a bana.

Jakadan Kasar Sin Hu Zhangliang, ya ce kasashen biyu sun kasance sun dade suna hadin gwiwa a bangare ilimi, yana mai cewa dalibai sama da 800 ne suka samu damarmakin karatu a kasar Sin karkashin shirin bada tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin.

Ya ce gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wani sabon shiri da ake kira "Tallafin karatu na kawancen Sin da Afrika", kuma daliban Saliyo 10 aka dauka a karkashinsa.

A nasa bangaren, ministan kula da ilmin gaba da sakandare na Saliyo, Aiah Gabkima, ya godewa gwamnatin kasar Sin bisa bayar da damar karatu ga 'yan asalin Saliyo.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka samu tallafin, su mayar da hankali ga karatun tare da zama wakilan kasar na kwarai a kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China